Snack's 1967
Basmalah 1
.

TAMBAYA MABUDIN ILMI |AMSAR TAMBAYOYIN KU A MUSULUNCI
JEKA KASA KASA SUNANKA
DA TAMBAYAN KA

Guestbook is loading comments...
|smsaiko sakocall me
Abdul Adamu sani HUKUNCE - HUKUNCIN DA SUKA KEBANTU GA MATA A GAME DA ADON JIKiN



1 Ana bukatar mace ta aikata abubuwan da suke sune halaye na cikar mutuntaka, wadanda suka kebantu da ita, kuma suka shafe ta.
Daga cikinsu a kwai yanke farce da gyara su, domin yanke farce sunna ce kamar yadda malamai suka yi ijma'i, kuma yanke farce tsafta ce, barin sa ya yi tsawo, ba a yanke ba, wannan abin muni ne kuma koyi da dabbobi ne.
Sa'anna farce yana boye datti, ya kuma hana ruwa saduwa da wani bangare na dan yatsa yayin alwala ko wanka.


Kuma sunna ne mace ta kawar da gashin hamata da na mara, domin yin aiki da hadisin da ya zo ingantacce akan haka.
Abin da ya fi shine ta yanke duk bayan sati ko kuma kada ya wuce kwana 40 ba ta yanke ba.

HUKUNCI NA BIYU. Abin da ake bukatar ta yi da gashin kanta, da gashin ido, da hukuncin yin lalle da tura gashi da shamfo.


* Ana bukatar mace ta raya gashin kanta, kuma haramun ne a gareta ta aske gashin sai dai in akwai larura. A Hadisin da Nasa'i da Bazzar suka ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya nuna haramun ne.
Amma idan ta dan yanke ko ta rage gashin, domin ta kasa bashi kulawar da ya kamata saboda yawansa, to babu laifi a gurin wasu Malamai. Zan ci gaba.
Domin wasu daga cikin matan Manzon Allah (SAW) sun aikata haka bayan mutuwar sa, saboda an hana su yin aure bayansa, don haka bas u da bukatar yin ado dag a shi.
Amma idan ta rage gashin domin koyi da kafirai da fasikai, ko kuma don ta kamuntu da maza, wannan haramun ne ba tare da shakka ba, domin an hana mata su yi koyi da kafirai, haka kuma an hana su, su kamantu da maza, idan kuma ta yi haka domin ado shi ma bai halatta ba. Don haka musulunci yana bukatar mace ta kiyaye gashin ta, ta kuma kula das hi, kuma an hana ta tara gashin kanta a saman ta yayi tozo, ko kuma ta tara shi a keyarta, domin kamar yadda Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya y ace hakan ko yi ne da matan kafirai.Imamu Muslim ya ya ruwaito hadisi, Manzon Allah (SAW) yana cewa"AKWAI WASU MATA DA ZA SU ZO KARSHEN ZAMANI, ZA A GANSU SUN SANYA TUFAFI, AMMA DUK DA HAKA TSIRANCIN SU A FILI YAKE, KUMA SUNA TAFIYA SNA KARAI-RAYA, KUMA ZA KA GA KAYUWAN SU KAMAR TOZON RAKUMI, Manzon Allah (SAW) yace"BA ZA SU SHIGA ALJANNA BA, KUMA BA ZA SU JI KO KANSHIN TA BA".
Kuma kamar yadda aka hana mace ta aske gashin kanta, ko ta rage shi ba tare da dalili ba, haka ma an hana hada shi, ko ta kara shi da wani gashin.
A hadisin da Imamul Bukhari ya ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya la'anci mata masu kara gashi da wadanda ake karawa.
Domin yin haka karya ce da yaudara.


(2). Ya haramta ga mace ta gusar da gashin idon ta ko na girarta, ko ta kawar da bangaren sat a kowace hanya, ta hanyar askewa ko yanke wa, ka ayi amfani da shaving powder, wannan duk haramun ne; domin Manzon Allah (SAW) ya la'anci mata ma su aikata haka da wadanda ake yi wa, haka kuma yin hakan canza halittar Allah ne, wanda Shaidan da ya yi shelan kuma yai alkawarin zai halarkar da'ya'yan Annabi Adamu ta hanyar ta, kamar yadda Alla (SWA) yak e gaya mana a cikin Suratul Nisa'I aya ta 119.
Haka nan yin shanfo ta hanyar kona gashi ko kuma amfani da sinadari, shima zai shiga layin wannan haramcin, domin shima wani nau'I ne na canza halittar Allah kuma koyi ne da kafirai.


(3). Haramun ne ga mace ko namiji, su cire hakori ko kuma a kankare tsakanin hakori da hakori domin abar fika, don nufin yin ado.Sai dai idan za a yi haka ne domin kawar da wani cuta (kamar a samu wani hakori ya fita daga layin jerin hakora) ko kuma saboda hakorin bashi da lafiya, to babu laifi, domin wannan zai shiga bangaren yin magani da kuma kawar da muni, sai dai ya kamata in mace zata yi haka ta samu likita kwararriya mace ko kuma namiji amintacce.

.
(4). Haramun ne mace ta yi zane a jikin ta, wanda ake sanya wani karfe a wuta sannan a yi zane da shi a jikin mace, sannan sai a sanya kwalli ko tawada a gurbin.Manzon Allah (SAW) ya la'anci wacce ta ke yi da wadda aka yi wa a jikinta.


Akwai cigaba
2017-02-16 01:02 · Reply · (0)


Online: Guests: 1


130095

SpeedCounter.net - Free web counter
Share Button